rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Lebanon Faransa Isra'ila

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Lebanon ta nemi agajin Faransa kan fadan Isra'ila da Hezbollah

media
Fira Ministan Lebanon Sa’ad al-Hariri. AFP

Fira Ministan Lebanon Sa’ad Hariri, ya nemi agajin Faransa, wajen dakile kazamin fadan dake shirin barkewa tsakanin mayakan Hezbollah dake kasar, da kuma Isra’ila.


Kiran na Lebanon ya zo ne bayan da Kungiyar Hezbollah ta yi ikirarin lalata wata tankar yakin Isra’ila, yayin wani farmakin makaman roka da ta kai cikin kasar, daga cikin Lebanon.

Tuni dai Isra’ilar ta sha alwashin maida martani kan harin na Hezbollah kan wata cibiyar sojinta dake kan iyakarta da Lebanon.

Tun a makon jiya, ake nunawa juna yatsa tsakanin Isra’ilar da mayakan na Hezbolla mai samun goyon bayan Iran, bayan da jagoran kungiyar Hassan Nasrullah ya sha alwashin maida raddi kan farmakin da Isra’ila ta kaiwa cibiyarsu dake birnin Beirut.