rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Hong Kong China Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Zanga-zanga ta tilasta rufe filin jragen saman Hong Kong

media
Masu zanga-zanga a yankin Hong Kong. REUTERS/Tyrone Siu

Zanga-zangar adawa da gwamnati dake ci gaba da gudana a Hong Kong ta tilasta dakatar da zirga-zirgar sauka da tashin jiragen sama a yankin, bayan da dubban masu zanga-zangar suka datse hanyoyin isa filin jiragen saman birnin.


Akalla safarar jiragen sama 16 aka soke a yau lahadi sakamakon zanga-zangar, wadda tun a jiya ta kazanta, bayan da aka yi arrangama tsakanin, gungun masu zanga-zangar da ‘yan sanda.

Kudurin dokar mika masu lafi daga yankin na Hong Kong zuwa China ne dai ya soma haddasa gagarumar zanga-zangar, wadda a yanzu ta rikide zuwa ta neman komawar yankin kan tsarin Dimokaradiyya irin na Turai, da samun karin yanzi daga China.