rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Myanmar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Musulman Rohingya na fuskantar kisan kare - dangi - MDD

media
Wasu 'yan gudun hijiran Rohingya a Bangladesh REUTERS/Rafiqur Rahman

Masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun ce musulmai yan asalin Rohingya da suka rage a Myanmar na fuskantar hadarin kisan kare dangi, suna kashedin cewa dawo da miliyoyin yan Rohingya gida zai yi wahala.


kwamitin bincike da hukumar kare hakkin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta kafa a shekarar da ta gabata, ya bayyana ayyukan da sojin suka yi a shekarar 2017 a matsayin kisan kare dangi.

Akalla yan Rohingya dubu 740 ne suka tsere daga kauyukan su sakamakon kona gidajen su da aka yi, wadda a ta dalilin haka ne aka kashe da dama daga cikin su, aka yi wa wasu fyade, wasu kuma suka fuskanci cin zarafi a sansanonin yan gudun hijirar Bangladesh inda suka nema mafaka.

Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce al’ummar Rohingya dubu 600, wadanda a halin yanzu ke makale a cikin jihar Rakhine na Myanmar na cikin halin ha’ula’i.

A binciken su na karshe kan barazanar da al’ummar Rohinyar ke fuskanta wadda zata gabatar gobe a birnin Geneva, Majalisar Dinkin Duniya ta ce Myanmar ta cigaba da kauda kai ga irin hallayar da ka iya kawo kisan kare dangi.