rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Isra'ila

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Netanyahu ya rasa rinjaye a zaben Isra'ila

media
Tuni Netanyahu ya fara neman hadin kan jam'iyyun adawa ko da dai kawo yanzu ba a da takaimaiman wanda zai iya zama Firaminista 路透社。

Firaministan Israila Benjamin Netanyahu ya gaza samun goyan bayan da ya ke bukata domin cigaba da zama a karagar mulki, kamar yadda sakamakon zaben da aka yi ya nuna, inda kawancen Jam’iyyun da Janar Benny Gantz ke jagorancin suka samu kujerun da suka dara na shi.


Sakamakon zaben ya nuna cewar masu kada kuri’u sun bijirewa Firaminista Benjamin Netanyahu, wanda yafi kowa dadewa a karagar mulkin Israila, wajen goyan bayan Janar Benny Gantz, wanda ya samu kujeru fiye da na Firaministan.

Alkaluma sun nuna cewar, kawancen Gantz na da kujeru 56 daga cikin Majalisar Israila mai kujeru 120, yayin da kawancen Netanyahu ke da kujeru 55.

Lura da yadda siyasar Israila take, wajen kulla kawancen jam’iyyu kafin sanin wanda zai jagoranci kasar, yanzu haka ana iya kwashe kwanaki ko makwanni kafin sanin wanda zai zama sabon Firaminista.

Yanzu haka kallo ya koma bangaren tsohon ministan tsaro Avidgor Lieberman wanda yaki goyan bayan Netanyahu wajen kafa gwamnati a zaben watan Afrilu, abinda ya tilasta zake gudanar da zabe ranar talata.

Lieberman da Janar Gantz duk sun bukaci kafa gwamnatin hadin kai, yayin da Netanyahu yace ba za shi taron Majalisar Dinkin Duniya da za’a fara makon gobe ba, domin fuskantar matsalar siyasar kasar.