rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Afghanistan Taliban Pakistan Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Afghanistan ta haramta zirga-zirgar manyan motoci a Kabul

media
Wasu sojojin Afghanistan yayin sintiri a birnin Kabul. REUTERS/Mohammad Ismail

Hukumomin tsaron Afghanistan sun dakatar da zirga-zirga, da kuma shigar manyan motoci cikin babban birnin kasar Kabul, domin dakile duk wani yunkurin kai hare-haren bam na kunar bakin wake, kafin ko kuma a lokacin zaben shugabancin kasar dazai gudana a gobe asabar.


A baya bayan nan, Taliban wadda ta kai munanan hare-haren kunar bakin wake, kan tarukan siyasa da ofisoshin jam’iyyu, ta fitar da wata sanarwar gargadin cewa duk wadda ya fita domin kada kuri’a a zaben na gobe, to fa ya kuka da kansa, kan duk abinda ya same shi.

To itama dai Pakistan dake makwabtaka Afghanistan ta bayyana tsaurara matakan tsaro akan iyakarsu har sai an kammala zaben shugaban kasar.

A yan makwannin nan mayakan Taliban sun yawaita yin amfani da manyan motoci makare da bama-bamai wajen kai hare-hare, inda a ranar 5 ga Satumban da muke ciki kungiyar Taliban ta halaka mutane 12 a Kabul, ta hanyar harin kunar bakin waken da babbar mota.

Cikin watan Mayun shekarar 2017 aka fuskanci harin kunar bakin waken da ba za a manta da shi ba a Afghanistan, wanda babbar mota tarwatse a kusa da ofishin jakadancin Jamus, inda rayuka sama da 150 suka salwanta, tare da jikkata daruruwa.