rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ana shirin kai mana hari kan albarkatunmu na Mai- Iran

media
Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani AFP/Iranian Presidency/HO

Ma’aikatar man fetur a Iran ta ce bayanan sirrin da ta samu na nuna cewa akwai yiwuwar kasar ta iya fuskantar hari na zahiri kan cibiyoyinta na man fetur ko kuma iya fuskantar kutsen na’ura.


Ministan man fetur na Iran Bijan Namdar Zanganeh ya ce ya zama wajibi kowanne sassa da ma’aikatun man fetur na kasar su kasance a ankare wajen iya fuskantar hari.

Zanganeh cikin sanarwar da ya wallafa a shafin ma’aikatar man fetur ta Iran, ya bayyana cewa za su shiryawa duk wata kasa da ke kokarin farmakarsu.

Amurka dai na zargin Iran da hannu kan harin da aka kaddamar kan cibiyoyin man Saudiya a watan nan da ya nakasa kashi 50 cikin dari na yawan man da kasar ke fitarwa Duniya, ko da dai Iran na ci gaba da musanta zargin.