rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

China

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Hadarin mota ya hallaka mutane 36 a China

media
Motar daukar marasa lafiya. REUTERS/Yuya Shino

Akalla mutane 36 ne suka mutu yayinda wasu kusan 40 kuma suka jikkata sanadiyyar hadarin wata motar safa a China wadda ta yi taho mu gama da motar dakon kaya.


Rahotanni sun bayyana cewa motar na dauke da mutane 69 akan hanyarta ta zuwa yankin gabashin Jiangsu da safiyar yau Lahadi, inda ta samu matsalar fashewar taya lokacin da take tsaka da tsala gudu bisa titi, matakin da ya kai ta ga karawa wata babbar motar dakon kaya.

Hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta China ta bayyana cewa, mutane 9 daga cikin 39 da suka samu raunuka na cikin mawuyacin hali, yayinda raunin mutane 26 ke da sassauci.

Bisa ga kididdiga dai cikin shekarar 2015 kadai, hadarin mota ya hallaka mutane dubu 58 a titunan kasar ta China.