rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
  • Palestinawa 22 hare-hare daga Israela ya kashe a Gaza.
  • Dan kunar bakin wake ya kashe mutun daya a ofishin 'yan sandan Indonesia

China Hong Kong

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Xi Jinping ya sha alwashin mutunta matsayin Hong Kong

media
Xi Jinping shugaban kasar China REUTERS/Thomas Peter

Shugaban kasar China Xi Jinping ya sha alwashin ci gaba da mutunta matsayi na musamman da Hong Kong ke da shi, dai dai lokacin da kasar ke shirin bikin cika shekaru 70 a gobe Talata, inda za a gudanar da faretin soji da kuma baje kolin sabbin makaman da kasar ke da su.


Dakarun soji 15,000 ake saran za su gudanar da fareti gobe talata a Dandalin Tiananmen, yayin da kasar za ta baje kolin sabbin makamanta na zamani domin duniya ta gani a wani yunkurin tauna tsakuwa da kuma nuna karfin da ta ke da shi.

Shugaba Xi Jinping ya bayyana cewar sannu a hankali gwamnatin China za ta ci gaba da aiwatar da shirin da ta ke da shin a China a matsayin kasa guda, mai tsari biyu a Hong Kong, inda ake cigaba da gudanar da zanga zangar neman yanci.

Shugaban ya ce suna da yakinin cewar da goyan bayan China da kuma Sinawa mazauna Hong Kong da Macau da ke da kishin kasar su, Hong Kong za ta samu ci gaba kamar yadda China ke samu.

An dai shirya jawabin shugaba Xi a wurin da aka yiwa lakabi da Kofar zaman lafiyar da shugaba Mao Zedong ya bayyana kafa sabuwar China ranar 1 ga watan Oktobar shekarar 1949.

Bayan faretin sojin yayin bukukuwan na gobe Talata, ana kuma saran fararen hula akalla 100,000 za su saki tattabaru 70,000 da balan balan 70,000 kafin wasan wutar da za’ayi.