rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

India

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Indiyawa sun daina bahaya a filin Allah Ta'ala

media
Indiyawa na fama da matsalar ban-dakuna domin bahaya RFI hausa

Firaministan India, Nerandra Modi ya ayyana kawo karshen matsalar bahaya a filin Allah Ta'ala a kasar mai yawan al’umma biliyan 1.3. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake bikin cika shekaru 150 da haihuwar Mahatma Ghandi da ya jagoranci nema wa kasar ‘yancinta daga turawan mulkin mallaka.


Firaminista Modi ya ce, a cikin watanni 60, kimanin Indiyawa miliyan 600 ne suka samu kebantattun ban-dakuna.

Mr. Modi wanda ya lashi takobin samar da wuraren bahaya a lokacin da ya fara darewa karagar mulki a shekarar 2014, ya ce, an gina ban-dakuna sama da miliyan 110 a sassan kasar.

Firaministan ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi ga wasu dagatan kauyuka su dubu 20 a yannkin yammacin Ahmedabab da ke jihar Gujarat, wato jiharsa ta asali kuma mahaifar uban kasar wato, Mahatma Ghandi da ke cika shekaru 150 da haihuwa.

Modi ya ce, daga yanzu, matan Indiya sun daina zaman jiran shigowar dare domin sassaka bahaya a filin Allah Ta'ala. kana ya ce, samar da ban-dakunan zai taimaka wajen kare rayuwar kananan yara.

Sai dai duk da wannan kokari da Modi ya yi na samar da wuraren bahayan, masharhanta sun ce, har yanzu akwai tarin miliyoyin ‘yan kasar da ba su da ban-dakunan.

A bangare guda, Mr. Modi wanda aka sake zaba a cikin watan Mayun wannan shekarar, ya kuma lashi takobin tsaftace India daga sharar robobi da ke gurbata muhalli nan da shekarar 2022.