rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
  • Palestinawa 22 hare-hare daga Israela ya kashe a Gaza.

Hong Kong China Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An haramtawa masu zanga-zanga rufe fuskokinsu a Hong Kong

media
Carrie Lam shugabar gwamnatin Hong Kong REUTERS/Amr Abdallah Dalsh

Shugabar gwamnatin Yankin Hong Kong Carrie Lam ta sanar da kafa dokar haramtawa masu zanga-zanga rufe fuskokinsu, kuma dokar  za ta soma aiki daga ranar Asabar 05 ga watan nan na Oktoba.


Wannan dai na daga cikin matakan da gwamnatin Hong Kong  kan shirin samar da wasu sabbin dokoki da za su kawo karshen tashin hankalin da yankin ke fuskanta, sakamakon zanga-zangar masu adawa da China da kuma neman komawa kan tsarin dimokaradiyar Turai.

A baya bayan nan dai sama da masu zanga-zanga 100 ne suka jikkata yayin arrangama da jami’an tsaro, bayan da ‘yan sandan suka harba musu kwanson hayaki mai sa hawaye dubu 1 da 400, harsasan roba 900 da kuma harsasai masu rai 6, bayan fahimtar aniyar masu zanga-zangar ta yi musu rotse.

Wannan na zuwa ne bayan da shugaban kasar China Xi Jinping ya sha alwashin ci gaba da mutunta matsayi na musamman da Hong Kong ke da shi, a yayin wani jawabi da yayi, lokacin da kasar ke shirin bikin cika shekaru 70, inda aka gudanar da faretin soji da kuma baje kolin sabbin makaman da kasar ke da su.