rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Korea ta Arewa Amurka Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ganawarmu da Amurka ta sake rushewa - Korea ta Arewa

media
Shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jong Un. Korean Central News Agency/Korea News Service / AP

Wakilan Korea ta Arewa da na Amurka sun tashi daga tattaunawar da suka ci gaba a ranar asabar kan warware shirin damarar nukiliyar kasar, da bayanai mabanbanta dangane da yadda ganawar ta gudana a Sweden.


Yayinda Korea ta Arewa ta ce tattaunawar ta sake rushewa ba tare da cimma yarjejeniya ba kamar yadda ta auku a watan Fabarairu, Amurka kuwa bayyana tattaunawar ta jiya tayi a matsayin babbar nasara.

Zalika Amurka ta bayyana amincewa da tayin Sweden na sake karbar bakuncin ci gaba da tattaunawarta da Korea ta Arewan nan da makwanni biyu.

Cikin watan Agustan da ya gabata Korea ta Arewa ta sake gwajin sabbin makamai masu linzami guda biyu karo na 5 cikin makwanni 2, a matsayin gargadi ga Amurka da kuma Korea ta Kudu kan atasayen hadin gwiwar da suke shirin gudanarwa.