Isa ga babban shafi
Faransa-Jamus-Turkiya

Faransa da Jamus sun yanke cinikin makamai tsakaninsu da Turkiya

Faransa ta sanar da dakatar da cinikin makamai tsakaninta da Turkiya biyo bayan bijirewa bukatar dakatar da hare-haren data kaddamar kan mayakan Kurdawa a arewacin Syria.

Dakarun Turkiya dana 'yan tawayen Syria, yayin shirin afkawa birnin Ras al-Ain a arewacin Syria dake karkashin ikon mayakan Kurdawa. 12 ga Oktoba, 2019.
Dakarun Turkiya dana 'yan tawayen Syria, yayin shirin afkawa birnin Ras al-Ain a arewacin Syria dake karkashin ikon mayakan Kurdawa. 12 ga Oktoba, 2019. Nazeer Al-khatib / AFP
Talla

Jamus ce dai ta soma bayyana irin wannan mataki kan kasar ta Turkiya da yammacin yau asabar.

Manyan kasashen Turan sun dauki matakin ne, bayan da dubban mutane a kasashen na Faransa da Jamus, suka gudanar da zanga-zangar adawa da hare-haren dakarun Turkiya kan mayakan Kurdawa a arewacin Syria.

Wadanda suka shirya zanga-zangar, sun ce sama da mutane dubu 20 ne suka fita gangamin a birnin Paris, yayinda a birnin Cologne a Jamus, sama da mutane dubu 10 suka shiga zanga-zangar.

Yayin gangamin, masu zanga-zangar dauke da launukan Kore, Ja da kuma ruwan dorawa, sun rika bayyana shugaban Amurka Donald Trump a matsayin mai zubar da jini, yayinda suke bayyana shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan a matsayin shugaban kungiyar IS na ainahi.

Ranar laraba, 9 ga watan Oktoba, 2019, dakarun Turkiya suka kaddamar da farmaki kan mayakan Kurdawan kungiyar YPG a arewacin Syria, wadanda Turkiyan ke kallo a matsayin yan ta’adda, kuma reshen haramtacciyar jam’iyyar Kurdawan kasar da ta dauki makamai domin kafa kasa mai cin gashin kanta.

Daya daga cikin manufar afkawa mayakan kurdawa da Turkiya tayi shi ne neman kafa wani katafaren yankin tsaro da za ta iya tsugunar da ‘yan gudun hijirar kasar Syria akalla miliyan guda, wadanda suka tsere zuwa Turkiyan bayan barkewar tashin hankalin yakin basasa.

Yanzu haka dai sabon fadan ya tilastawa sama da fararen hula dubu 100 tserewa daga muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.