Isa ga babban shafi

Zanga-Zangar Hong Kong ta dauki sabon salo

Dubunnan masu zanga-zangar adawa da gwamnati a Hong Kong sun bijirewa hakuma game da haramcin gangamin da ‘yan sandan kasar suka musu, bayan matakin jami’an tsaron na dukan kawo wuka kan wasu daga cikin masu zanga-zanga baya ga dabawa jagoransu wuka.

Masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a Hong Kong.
Masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a Hong Kong. REUTERS/Ammar Awad
Talla

A wannan karon masu zanga-zangar ta Hong Kong sun fantsama hatta a sassan da a baya aka haramta musu shiga wato yankunan da ke karbar baki ‘yan yawon bude ido don nuna fushinsu kan yunkurin kashe jagoransu Jimmy Sham wanda aka dabawa wuka a wuya da ciki ranar Laraba.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani daga bangaren gwamnati kan wanda ke da alhakin yunkurin kashe jagoran zanga-zangar wadda ke yunkurin kifar da gwamnatin yankin mai ra’ayin China, sai dai akwai bayanan da ke nuna cewa zanga-zangar a wannan lokaci ka iya munana fiye da ta baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.