rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Hong Kong China

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An yanke kunnen wani dan siyasa a Hong Kong

media
Shugabar gwamnatin Hong Kong Carrie Lam REUTERS/Umit Bektas

Masu zanga – zanga a Hong Kong sun nuna alamun cewa suna iya fitowa gangami a yau Lahadia manyan shagunan sayar da kayayyakin masarufi, mako daya bayan makamancin gangamin ya rikide zuwa tarzoma tsakaninsu da ‘yan sanda.


A karshen makon da ya gabata masu zanga – zangar kin jinin gwamnatin yankin suka yi cincirindo a wani katafaren shago, yayin da wani mutun ya ratsa taron da sharbebiyar wuka, inda har ma ya yanki rabin kunnen wani dan siyasa.

An shirya wasu jerin gangamin a saura biranen yankin, don nuna rashin amincewa da halayyar ‘yan sanda da katsalandar da suke zargin China da yi a harkokin siyasar kasar.