Isa ga babban shafi
Hong Kong

An cinnawa mutum wuta yayin zanga-zanga a Hong Kong

Wani jami’in ‘yan sandan Hong Jong ya harbe daya daga cikin masu zanga-zangar neman tabbatar da dimokradiya a yankin, yayin da a gefe guda aka cinna wa mutum guda wuta sakamakon husumar da ta barke tsakaninsa da wani.

Daya daga cikin masu zanga-zanga a Hong Kong, bayan shiga hannun 'yan sanda 11/11/2019.
Daya daga cikin masu zanga-zanga a Hong Kong, bayan shiga hannun 'yan sanda 11/11/2019. REUTERS/Tyrone Siu
Talla

Masu zanga-zangar sun mayar da martani kan harbin da aka yi wa dan uwansu a sanfin safiyar wannan Litinin, inda suka tayar da hatsaniya a tashoshin jiragen kasa tare da datse tituna baya ga farfasa shaguna.

A daidai lokacin da aka yi harbin ne wani mahari rufe da fuskarsa ya cinna wa wani mutum wuta bayan ya tiltila masa wani abu mai kama da man fetur a jiki, yayin da aka nadi hoton bidiyon wannan al’amari mai tayar da hankali kuma aka watsa kai tsaye ta kafar Facebook.

Jami’an ‘yan sanda sun ce, daya daga cikin masu zanga-zangar ne ya kai wannan harin bayan wata ‘yar gadama ta kaure a tsakaninsu.

Shugabar yankin Hong Kong Carrie Lam ta gabatar da taron manema labari, inda ta yi tur da tashin hankalin da ya faru, tana mai jaddada cewa, ba za ta bayar da kai bori ya hau ba.

A halin yanzu dai, mutumin da dan sandan ya harba na cikin mawuyacun hali a asibiti kuma a karo na uku kenan da ake amfani da harsashin gaske wajen harbin masu zanga-zangar wadanda suka kwashe makwanni 24 suna bore.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.