Isa ga babban shafi

Netanyahu na fuskantar tuhumar cin hanci da rashawa a Isra'ila

Babban Lauyan gwamnatin Israila ya zargi Firaminista Benjamin Netanyahu da laifin cin hanci da rashawa da almundahana da kuma zamba cikin aminci, matakin da ake ganin na iya kawo karshen siyasar sa.

Franministan Isra'ila Benyamin Netanyahu yayin wani jawabi ga 'yan kasar
Franministan Isra'ila Benyamin Netanyahu yayin wani jawabi ga 'yan kasar REUTERS/Ronen Zvulun
Talla

Ma’aikatar shari’ar Israila tace Babban lauyan gwamnati Avichai Mandelblit ya amince ya gurfanar da Firaminista Benjamin Netanyahu a gaban kotu saboda zargin karbar cin hanci da almundahana dakuma zamba cikin aminci.

Ma’aikatar tace tuni aka gabatar da takardun karar ga lauyoyin Firaministan, wadanda suka hada da karbar kyaututtuka taba da giya da kayan kawa na mata da kudin su ya kai Dala 200,000 domin taimakawa masu kyautar.

Wannan zargi dai ba zai hana Netanyahu cigaba da rike kujerar sa ba, har sai an kammala sauraron shari’ar da za’ayi masa, amma kuma yana iya matsin lamba a gare shi saboda nauyin zargin.

Masu sa ido a siyasar kasar na cewa, Firaministan na iya rokon Majalisar dokoki ta bashi kariyar hana tuhumar sa a gaban kotu, har sai ya sauka daga mukamin sa, duk da yake babu tabbacin yana iya samun haka.

Israila ta kwashe kusan shekara guda yanzu haka ba tare da gwamnati ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.