Isa ga babban shafi

Tara makaman nukilya ba zai kawo zaman lafiya a duniya ba - Fafaroma

A Lahadin nan shugaban darikar Katolika na duniya, Fafaroma Francis ya caccaki dabi’ar amfani da makaman nukiliya da kuma yadda cinikin makamai ke habaka, yayin da yake bayyana alhini tare da girmamawa ga wadanda hari da makamin ya shafa a Nagasaki na Japan.

Fafaroma Francis, tare da Bishop - Bishop na Vatican a birnin Tokyo.
Fafaroma Francis, tare da Bishop - Bishop na Vatican a birnin Tokyo. © Reuters
Talla

A wata ziyarar mai mahimmanci a birnin Nagasaki na kasar Japan da makamin nukiliya ya daidaita a watan Agustan 1945, Francis ya ce amfani da makamin nukilya ba zai taba kawo zaman lafiyar da ake nema a duniya ba.

Akalla mutane dubu 74 ne suka mutu bayan Amurka ta yi amfani da makamin a birnin da ke yammacin Japan, kwanaki uku bayan makamanci harin ya lakume rayukan mutane dubu dari da 40 a Hiroshima.

A jawabin sa, Fafaroma ya ce laifini amfani da makamin nukiliya, watahaduwa mai sosa rai da ya yi da wadanda suka tsira daga harinda aka kai Hiroshima shekaru kusan 70 da suka wuce.

Wadanda suka tsira daga wannan harin a Hiroshima, sun yi kira ga al’ummar duniya da kada ta manta da irin barnar da harin ya haifar.

Sun shaida wa Fafaroman irin bala’in da suka gani yayin kazamin harin da ya lakume rayuka dubu 140, ya kuma nakasa da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.