Isa ga babban shafi
Iraq

Firaministan Iraqi zai yi murabus

Firaministan Iraqi Adel Abdel Mahdi a  Juma’ar nan ya ce zai mika takardar murabus ga majalisar dokokin kasar sa’o’i bayan jagoran mabiya mazabahar Shi’a ya yi kira da a janye goyon bayan da ake ba shi a majalisar, yayin da zanga zanga ta yi kamari a kasar, inda a waje daya rahotanni ke cewa yawan mutanen da aka kashe a garin Nasiriyya a yau sun kai 15.

Firaministan Iraqi Adel Abdel Mahdi a Bagadaza.
Firaministan Iraqi Adel Abdel Mahdi a Bagadaza. Iraqi Parliament Office/Handout via REUTERS
Talla

Bayan mutane da dama sun mutu a zanga – zangar da ke ci gaba da rincabewa, jagoran Shi’a, Ayatollahi Ali Sistani ya bukaci illahirin ‘yan majalisar zartasawa su yi murabus, yana mai kira da a janye goyon bayan da ake ba su.

A hudubarsa ta wannan Juma’a, Ali Sistani ya yi caccaka kan yadda al’amura suka ci gaba da yamutsewa a kasar.

Sa’o’i bayan wannan kiran da jagoran ‘yan shi’an ya yi ne, Firaminista ya Adel Abdel Mahdi ya bayyana aniyarsa ta mutunta bukatun al’ummar kasar da na jagoran addini, bayan kusan watanni 2 na mummunar zanga – zanga da ta lakume rayuka 400.

Wannan bayani na Mahdi ya kasance wani babban albishir ne ga dimbim masu zanga zanga da suka taru a dandalin Tahrir don yin tir tare da nuna kin jinin gwamnatin da suke wa kallon gwana wajen rashawa, baya ga rashin sanin makaman aiki, inda suka buge da kade – kade da bushe - bushe.

A halin da ake ciki, tsohon Firaminista, kuma dan majalisar dokoki, Haider al-Abadi ya yi kira ga ‘yan majalisar dokoki da su fito a wannan Asabar don kafa sabuwar gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.