Isa ga babban shafi
Hong Kong

Masu zanga - zanga a yankin Hong Kong sun sake yin fitar dango

Masu zanga – zangar neman kafa dimokaradiyya a Hong Kong sun yi fitar dango a titunan yankin a Lahadi nan, a wani gagarumin gangami, inda har wani babban dan gwagwarmaya ke yi wa jagorori masu bada hadin kai ga China kashedin cewa su na da dama ta karshe ta kawo karshen rikicin siyasar yankin.

Masu zanga-zangar yankin Hong Kong.
Masu zanga-zangar yankin Hong Kong. REUTERS/Heo Ran
Talla

Jagororin wannan gangamin dai sun yi kiyasin cewa akalla mutane dubu dari 800 suka yi jerin gwano na tsawon sa’oi’ a babban birnin yankin, wanda ya yi fice a harkar kasuwanci a duniya, yayin da ake cika watanni 6 da soma wannan zanga – zangar da ke neman fitar da yankin daga hayyacin sa.

‘Yan sandan birnin, wanda bisa al’ada sun saba kawo adadin masu zanga – zanga sabanin wanda jagororin gangamin ke bayarwa, sun shaida wa kafofin yada labarai a yankin cewa wandanda suka fito ba su zarce dubu dari da 83 ba, sai dai wannan adadin da suka bayar ma ya zarce wadanda suka taba bayarwa a baya.

Wannan gangamin dai ya samu izini na ba sa bambam daga ‘yan sanda, kuma yana zuwa ne makonni 2 bayan da jam’iyyun da ke goyon bayan gwamnati suka sha dukan kawo – wuka a zabukan kananan hukumomi, lamarin da ke watsi da ikirarin gwamnati na cewa mafi rinjayen al’ummar yankin ba sa goyon bayan zanga – zangar.

Da dama daga cikin masu zanga – zangar da suke sanye da bakaken tufafi cikin fushi, sun bayyana takaicinsu da yadda shugabar yankin Carrie Lam ta soke yiwuwar duk wata tattaunawa da za ta kai ga samun mafita, ta wurin cewa ba za ta bada kai bori ya hau ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.