Isa ga babban shafi
India

Zanga-zanga kan dokar damar zama dan kasa ta kazanta

Amurka da Birtaniya sun gargadi ‘yan kasashensu da su kaucewa ziyartar arewa maso gabashin India, inda, zanga-zanga ta kazanta kan adawa da dokar baiwa bakin haure damar zama ‘yan kasa da kuma haramtawa bakin Musulmai a Indian samun damar.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a arewa maso gabashin India.
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a arewa maso gabashin India. AFP
Talla

Masu adawa da dokar dai na fargaba dangane da dokar ta fuskoki da dama, ciki har da baiwa ‘yan ci rani damar mamaye ayyukanyi fiye da ‘yan kasa a Indian, sai kuma haddasa rarrabuwar kai tsakanin mabiya addinai daban daban da kuma Musulmi.

Dubban masu zanga-zanga ne suka yi ftar dango yau asabar babban birnin kasar New Delhi, yayinda a jihar West Bengal zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali, inda aka kone tashohin jiragen kasa 2 da kuma manyan motocin safa 20.

Ranar alhamis din da ta gabata, Majalisar dokokin India ta amince da kudirin dokar da ta ba da damar zama dan kasa ga bakin haure daga wasu kasashen ketare wadanda ba musulmai ba, yayin da gwamnatin kasar ta girke daruruwan dakaru a arewa maso gabashin kasar, sakamakon mummunar tarzomar da ta tashi saboda dokar.

Dokar za ta bai wa gwamantin India damar bada takardar zama dan kasa ga miliyoyin bakin-haure da suka shiga kasar ba bisa ka’ida ba daga kasashe 3 da ke makwabtaka da ita, gabanin shekarar 2015, muddin su ba muslmai ba ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.