rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

China Korea ta Kudu Japan Korea ta Arewa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashen China Japan da Korea ta kudu na taro kan Korea ta Arewa

media
Shugaba Kim Jong-un na Korea ta Arewa. KCNA VIA KNS / AFP

Kasashen China Japan da Korea ta kudu na wani taron hadin gwiwa da China ke karbar bakonci yau Talata, taron da ke da nufin hadin kan kasashen dama yadda za su bullowa makwabciyarsu Korea ta Arewa.


Taron wanda ke gudana a birnin Chengdu na kudu maso yammacin China na zuwa ne a daidai lokacin da wa’adin alkawarin kyautar Kiristimeti da shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un ya yi ke daf da cika, wanda yasa ake ganin taron na da nasaba da kalaman na Kim Jong Un.

Kasashen 3 dai wadanda ke matsayin makusanta ga Korea ta Arewa musamman China da ake kallo a matsayin uwar gijiyarta, kalaman na Kim tun cikin watan jiya ya tayar da hankulansu bisa tsoron kada alkawarin ya zamo karkashin shirin kasar ne na makaman nukiliya.

Kim Jong Un, a tun daga bara suka fara dasawa da Donald Trump na Amurka, ya yi alkawarin bayar da kyautar Kristimati, kyautar da bai fayyace abin da ta kunsa ba, ko da dai masharhanta na ganin ba zai wuce wani sabon gwajin makamin nukiliya ba.