Isa ga babban shafi
Iraqi-Amurka

Masu zanga-zangar Iraqi sun farmaki Ofishin jakadancin Amurka

Dubun dubatar masu zanga-zanga a Iraqi sun farmaki Ofishin jakadancin Amurka yau Talata bayan farmakin jiragen yakin Amurkan a karshen mako kan sansanin sojin da ke samun goyon bayan Iran a cikin kasar ta Iraqi da ya kashe akalla mayakn Hezbollah 25.

Masu zanga-zangar Iraqi a Ofishin jakadancin Amurka.
Masu zanga-zangar Iraqi a Ofishin jakadancin Amurka. REUTERS/Thaier al-Sudani
Talla

Masu zanga-zangar ciki har da Mata Maza da kananan yara suna daga tutocin kungiyar ta Hezbollah ne suka isa yankin da Ofishin jakadancin na Amurka ya ke, yankin mafi karfin matakan tsaro a birnin Baghdad.

Yayin boren na yau dai masu zanga-zangar sun rika kona tutocin Amurka tare da furta kalamai masu zafi ga gwamnatin ta Amurka, matakin da ya tilasta girke jami'an tsaro da nufin tarwatsa su ta hanyar harba musu hayaki mai sanya hawaye da ruwan zafi.

Farmakin masu zanga-zangar na zuwa dai dai lokacin da gwamnatin Iraqi ke cewa ya zama wajibi ta yi nazari a game da alakar da ke tsakaninta da Amurka, bayan da jiragen yakin kasar ta Amurka suka kai farmaki kan sansanin mayakan da ke samun goyon bayan Iran a cikin kasar ta Iraki.

Sanarwar da gwamnatin kasar ta Iraki ta fitar, ta bayyana harin a matsayin wanda aka kai saboda dalilai na siyasa amma ba domin al’ummar Iraki ba, abin da ke nufin cewa ya zama wajibi a yi nazari tare da daukar mataki dangane da lamarin.

Sanarwar ta ce harin ba wani abu ba ne face keta hurumin Iraki a matsayinta na kasa mai cikakken ‘yanci sannan kuma ya yi hannun riga da manufofin rundunar kawance da kasashen duniya suka kafa don yaki da ayyukan ta’addanci a yankin.

Washe garin wannan hari da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 25 da raunata wasu 51, an samu barkewar zanga-zanga a cikin kasar ta Iraki, yayin da aka samu rahotannin kona tutar Amurka.

A martanin da ta fitar dangane da lamarin, ma’aikatar harkokin wajen Rusha, ta bayyana musayar wuta tsakanin Amurka da Hezbollah a matsayin abin asha, yayin da ita kuma Iran ta bayyana harin a matsayin wata alama da ke tabbatar wa duniya cewa Amurka na goya wa ta’addanci baya ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.