Isa ga babban shafi
Taiwan

Babban kwamandan sojin Taiwan ya mutu a hatsari

Babban kwamandan askarawan Taiwan, Janar Shen Yi-ming ya mutu sakamakon hatsarin da wani jirgi mai saukar angulu ya yi a safiyar yau Alhamis, kuma tare da shi akwai wasu Janar-Janar biyu na rundunar sojin kasar.

Mutane biyar sun tsira da rayukansu a hatsarin jirgin mai saukar angulu
Mutane biyar sun tsira da rayukansu a hatsarin jirgin mai saukar angulu REUTERS THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY
Talla

Ma’aikatar tsaron Taiwan ta ce, jirgin ya yi hatsari ne lokacin da yake dauke da mutane 13 a wani wuri mai cike da tsaunuka a yankin arewa maso gabashin kasar.

An yi nasarar ceto mutane biyar da ransu bayan an tura tawagar sojoji ta musamman jim kadan da aukuwar lamarin.

Janar Shen mai shekaru 62 da sauran jami’an na kan hanyarsu ce ta zuwa ziyartar sojojinsu da ke Yilan, yayin da ibtila’in ya rutsa da su a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaben shugabancin Taiwan.

Shugabar Taiwan, Tsai Ing-wen ta ce, ta soke duk wani yakin neman zabe na tsawon kwanaki uku domin nuna alhinin wannan gagarumin rashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.