Isa ga babban shafi
Syria

Adadin rayukan da suka salwanta a yakin Syria ya zarta dubu 380

Kungiyar 'Syrian Observatory' dake sa ido kan yakin kasar ta Syria, ta fitar da sabuwar kididdigar adaddin wadanda suka halaka a yakin kasar da a yanzu ke shirin shiga shekaru 9 da barkewa.

Dubban rayuka na ci gaba da salwanta a yakin Syria.
Dubban rayuka na ci gaba da salwanta a yakin Syria. AFP/File
Talla

Sakamakon kididdiga ta karshe da kungiyar ta fitar a watan Maris na bara dai ya nuna cewar yakin na Syria na lakume rayukan sama da mutane dubu 370, to amma a yau asabar, sabuwar kididdigarta nuna adadin ya zarta mutane dubu 380, ciki harda fararen hula dubu 115.

Zuwa yanzu kuma bincike ya tabbatar da cewar yakin na Syria ya tagayyara sama da ‘yan kasar miliyan 13, ciki harda wadanda ke gudun hijirar dole a kasashen ketare.

A jimlace kuma yakin ya lakume rayukan mayakan ‘yan tawaye, Kudawa da kuma masu ikirarin jihadi samada dubu 69, sai kuma mutane dubu 88 da suka halaka yayinda suke tsare a gidajen Yari, ko kuma bayan sace su daga bangarorin dake yakar juna a Syrian.

A bangaren ‘yan ta’adda kuwa, wadanda ke sa idanu a yakin Syrian sun ce sama da mayakan IS da na kungiyar Tahrir al-Sham dubu 67 suka halaka a yakin, yayinda a bangaren sojoji, jimillar dubu 128 suka halaka, fiye da rabinsu sojin Syria, sai kuma mayakan Hezbollah dake tallafa musu a yakin da ya barke a shekarar 2011.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.