Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 43 a Indonesia
Ambaliya da zabtarewar kasa a Indonesia sun haddasa mutuwar mutane 43,inda wasu dama suka bata.Iftila’in da afkawa Jakarta a kasar ta Indonesia na daga cikin mafi muni da suka auku a yankin tun bayan shekara ta 2013 da suka haddasa mutuwar duban mutane.
Wallafawa ranar:
Gwamnati ta aike da jami’an kiwon lafiya dake ta gargadin jama’a wajen tsaptace ruwan sha da muhalin su don kaucewa kamuwa da cutuka.
Sama da mutane dubu 192 suka canza matsuguni,inda gwamnatin ta samar musu wuraren zama na gajeren lokaci, unguwani da dama ne yanzu haka suka shafe.
Kungiyoyin agaji na ci ga da aikewa da kayaki zuwa jama’a dake cikin yanayi mara kyau.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu