Isa ga babban shafi
Amurka-Iran

Trump ya gargadi Ayatollah Khamne'i kan yiwa Turai barazana

Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi jagoran juyin-juya halin Iran Ayatollah Ali Khamenei kan kalamansa na jiya juma’a da ke zargin Washington da rura wuta kan kuskuren harbor jirgin Ukraine da Iran ta yi dama batun nukiliyar kasar baya ga sabbin takunkuman da Trump ya sake laftawa Tehran.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. Reuters
Talla

Cikin sakon Twitter da Trump ya wallafa ya gargadi Khamnei da ya kula da kalamansa, kan barazanar da ya ke kokarin yiwa Amurkan da nahiyar Turai dungurugum, yana mai cewa babban kuskurene yadda Khamene'i ya bayyana kasashen Faransa, Birtaniya da kuma Jamus a matsayin ‘yan amshin shata ga Amurkan.

Cikin kalaman na Trump ya ce maimakon Khamnei ya tsaya tsara kalamai don muzanta kasashen kamata ya yi, yayi tunanin halin da tattalin arzikin kasarsa ke ciki da kuma rigingimun da ke gabanta baya ga halin matsin rayuwar da al’ummarsa ke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.