Isa ga babban shafi
Yemen

Farmakin 'yan tawayen Houthi ya hallaka Sojin Yemen 83

Sanarwar ma’aikatun Lafiya da na tsaro a Yemen sun tabbatar da kisan Sojin kasar fiye da 80 a wani farmakin makami mai linzami da jirage marasa matuki da ‘yan tawayen Houthi suka kaddamar a jiya Asabar.

Mayakan 'yan tawayen Houthi na Yemen.
Mayakan 'yan tawayen Houthi na Yemen. REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

Harin na jiya Asabar ya kawo karshen zaman lafiya na ‘yan watanni da bangarorin biyu suka yi ba tare da farmakar juna ba tsakanin ‘yan tawayen na Houthi masu samun goyon bayan Iran da kuma halastacciyar gwamnatin kasar mai samun goyon bayan Saudiyya da hadakar Sojin kasashen Larabawa.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan tawayen na Houthi sun farmaki wani masallachi ne lokacin da ake tsaka da sallah a sansanin sojin gwamnati da ke yankin Marib mai tazarar kilomita 170 da Sanaa babban birnin kasar.

Sanarwar ma’aikatar lafiya a birnin Sanaa ta ce Soji 83 suka mutu sanadiyyar farmakin yayinda wasu 148 suka jikkata, harin da aka bayyana da mafi muni da ya lakume rayukan jama’a tun bayan faro yakin kasar a shekarar 2014.

Wata majiya ta bayyana cewa tuni bangaren Sojin na gwamnati da hadakar Sojin dakarun kawancen kasashen larabawa suka mayar da martani kan harin wanda kawo yanzu ba a bayyana adadin mayakan Houthi da suka mutu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.