rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

China Amurka Lafiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An gano mutum daya dauke da cutar SARS a Amurka

media
Likitoci a yankin Wuhan na kasar China REUTERS/Stringer

Mutane akalla 9 ne suka rasa rayukan su sanadiyyar bular cutar mura a wani yankin kasar ta China.

Mutane 400 suka kamu da cutar, kuma kamar yadda hukumomin kasar ke cewa suna daukan matakan dakile ta, ganin yadda take ta yaduwa.


Shugaban China a wani sako da aike ga al’uma ya bukaci yan kasar da su dau matakan da suka dace wajen aiki da matakan kariya, jami’an kiwon lafiya a kasar sun mayar da hankali wajen tattance mutanen da suka kamu da wannan kwayar cuta.

Wasu kasashen Duniya sun soma mayar da hankali ga matafiya daga China, a Amurka an gano mutum daya dake dauke da kwayar cutar, lamarin da Hukumar lafiya ta Duniya take shirin gudanar da taro a kai domin duba irin matakan da ya dace kasashen Duniya su dauka don kawo karshen kwayar cutar.