Isa ga babban shafi
China-Corona

An samu karuwar mutanen da suka kamu da cutar Corona a China

Hukumomin lafiya a China sun ce adadin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus da aka fi sani da murar mashako ya kai mutum dubu 28 da 18 bayan da a baya-bayan nan aka samu karin mutum dubu 3 da 694 da aka tabbatar sun kamu da cutar.

Asibitin da ake kula da masu dauke da cutar murar mashako a yankin Wuhan na China.
Asibitin da ake kula da masu dauke da cutar murar mashako a yankin Wuhan na China. Hector RETAMAL / AFP
Talla

Bayanan da hukumar ke gabatar wa kowacce rana sun nuna cewar an samu karin mutuwar mutane 73 akasarin su daga yankin Hubei da kuma wasu yankuna guda 3, abinda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa 563.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce suna aiki tukuru don shawo kan cutar wadda yanzu haka ta watsu zuwa wasu kassahen duniya kuma take barazana hatta ga tattalin arziki da kasuwancin kasa da kasa.

Sai dai WHO ta bayyana cewa akwai bayanan karya da wasu ke yadawa kan cutar wadda ta ce har yanzu bata matsayin babbar barazana ga duniya yayinda ta sha alwashin wayar da kan jama'a game da bayanan karyar musamman a kafofin sada zumunta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.