Isa ga babban shafi
Iran

Iran na bikin cika shekaru 41 da juyin-juya hali

Yayin bikin cika shekaru 41 da juyin-juya halin Iran, shugaban kasar Hassan Rouhani a jawabinsa gaban dubun-dubatar al’ummar da suka yi dandazo a dandalin Azadi na birnin Tehran ya caccaka Amurka da Shugaba Donald Trump dama wadanda ke yiwa tsare-tsaren kasar zagon kasa musamman a yankin gabas ta tsakiya.

Dubun dubatar al'ummar Iran da ke halartar bikin cika shekaru 41 da juyin-juya halin kasar.
Dubun dubatar al'ummar Iran da ke halartar bikin cika shekaru 41 da juyin-juya halin kasar. Nazanin Tabatabaee/WANA (West Asia News Agency) via REUTERS
Talla

Yayin taron na cika shekaru 41 da kafa Jamhuriyyar ta Iran bayan kawo karshen mulkin sarki Shah, daruruwan mahalarta taron sun rika daga hoton jagoran juyin-juya halin kasar Rouhullah Khomeiny da Ayotollahi Ali Khamnei yayinda a bangare guda matasa suka rika kona tutar Amurka.

Dubun dubatar al’ummar kasar ta Iran da suka yi dandazon tunawa da ranar mai matukar tarihi, sun kuma yi tofin alatsine ga kasashen Amurka Isra’ila da Saudiya baya ga watsi da shirin zaman lafiyar gabas ta tsakiya da Donald Trump ya gabatar.

Alaka ta kara tsami tsakanin Amurka da Iran ne bayan kisan baya-bayan nan da Sojin Amurkan suka yiwa babban kwamandan Sojin Iran a ketare Qassem Soleimani a Iraqi, inda martanin Iran ya kai ga harba makamai masu linzami 22 kan sansanin Sojin Amurka da ke Iran.

Cikin jawabinsa a wajen taron Shugaba Hassan Rouhani ya bayyana cewa har yanzu Amruka da ke ikararin karfi a duniya ta gagara yardawa kanta tare da amincewa da nasarar da juyin juya halin da al’ummar Iran suka samu dama bunkasa da girman kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.