Isa ga babban shafi
Syria

Fararen hula dubu 900 sun tagayyara a arewacin Syria

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane dubu 900 sun rasa muhallansu sakamakon hare-haren dakarun kawancen Syria da Russia kan ragowar mayakan ‘yan tawaye a lardin Idlib dake arewa maso yammacin kasar, tun daga watan disamba na bara kawo yanzu.

Sansanin 'yan gudun hijirar Syria dake lardin Idlib a arewacin kasar.
Sansanin 'yan gudun hijirar Syria dake lardin Idlib a arewacin kasar. www.syriahr.com
Talla

Rahoton majalisar ya kuma ce jarirai da kananan yara na ci gaba da mutuwa saboda matsalar cinkoso a sansanonin ‘yan gudun hijira a dai dai lokacin da ake tsananin sanyi a arewacin kasar ta Syria.

Shugaban hukumar agajin majalisar dinkin duniya Mark Lowcock, ya ce rikicin yankin arewa maso yammacin kasar ta Syria yayi matukar muni, ganin cewa da farko kididdigar da majalisar ta fitar ta nuna adadin mutanen da fadan ya tagayyara ya kai dubu 100, amma a yanzu ya kai kimanin dubu 900.

Shugaban yace da dama daga cikin wadanda lamarin ya shafa mata da kananan yara ne wadanda suka shiga wani hali na kaduwa, lamarin dake tilasta musu kwanciya a fili saboda matsalar cinkoso a sansanonin duk kuwa da wani yanayi na tsananin sanyi da ake fama da shi.

Rahoton yace iyaye na daukar matakin kona robobi dan taimakawa ‘ya’yansu domin jin dumi, sai dai kananan yara da ma jarirai na ci gaba da mutuwa sakamakon tsananin da suke fuskanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.