Isa ga babban shafi

Fasinjoji da aka killace saboda Coronavirus sun fitce daga jirgin Japan

Daukacin mutanen da ke cikin jirgin ruwan yawan bude ido mai suna Diamond Princess, sun fice daga jirgin bayan share tsawon makonni biyu ana killace da su don hana yaduwar annobar cutar murar mashako ta Coronavirus a gabar ruwan kasar Japan.

Jirgin ruwan yawo bude ido na Diamond Princess
Jirgin ruwan yawo bude ido na Diamond Princess Reuters
Talla

Fasinjoi sama da 500 ne suka fice daga jirgin a safiyar Laraba, bayan da aka tabbatar da cewa babu wanda ke dauke da kwayar cutar mai saurin yaduwa.

Wannan jirgin ya isa gabar ruwan kasar Japan ne dauke da fasinjoji 3,700 a daidai lokacin da cutar ta tsananta, lamarin da ya tilastawa mahukunta daukar matakin kebe illahirin mutanen da ke cikinsa don yi masu gwaji.

Bayan share tsawon kwanaki 14, an tabbatar da cewa mutane 542 daga cikinsu na dauke da kwayar cutar ta Coronavirus ko COVID-19. Sabbin alkaluma a game da adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar sun haura mutane dubu biyu a halin yanzu.

Lura da tsanantar wannan cuta ne gwamnatin Rasha ta bakin mataimakiyar firaministan kasar Tatiana Golikova ta sanar da matakin hana ‘yan asalin China shiga kasar daga ranar Alhamis, matakin da zai shafi ma’aikata, masu yawon bude ido da kuma dalibai. Kasashen biyu dai na da iyaka mai tazarar kilomita dubu 4 da 250 a tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.