rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Barayin Shanu sun hallaka mutane 30 a Zamfara

Barayin shanu sun hallaka akalla mutane 30 a wasu jerin hare-hare da suka kai kan wasu kauyukan jihar Zamfara da ke karamar hukumar Maradun a yammacin ranar Talata. Wani shugaban al’umma a kauyen Gyadde Jabbi Labbo ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, barayin shanun sun kai samamen bisa Babura inda suka yi awon gaba da tarin dabbobi, a kauyukan da da suka hada da Sakkida, Farin Zare, Orawa, Gyadde da kuma Sabon Gari.