Jam’iyyar adawa a Jamaica ta lashe zabe
Babbar Jam’iyyar adawa a kasar Jamaica, ta People’s National Party, ta lashe zaben kasar da aka gudanar, wanda batun tattalin arzikin kasa ya mamaye yakin neman zabenta.
Wallafawa ranar:
Wannan nasarar da Jam’iyyar ta samu na nuna cewa, shugabanta Portia Simpson Miller, zata koma matsayinta na Fira Minista.
Tuni dai Jam’iyyar Labour mai mulki ta amsa shan kaye a zaben.
Uwar gida Simpson Miller mai shekaru 66, an fara zabenta a Majalisar kasar a shekarar 1976, kuma it ace mace ta farko matsayin Fira minista tsakanin shekarar 2006-2007.
Akwai dai Kalubale babba da ke a gabanta game da bashin da ake biyar kasar tare da matsalar rashin aikin yi da ke addabar ‘yan kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu