rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Cambodia Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotu ta yanke wa Khmer Rouge hukuncin daurin rai da rai a Cambodia

media
Khmer Rouge a lokacin ya ke gurfana gaban kuliya Reuters

A yau Juma’a, wata kotun Majalisar Dinkin Duniya ta yanke hukuncin daurin raid a rai ga Khmer Rouge wani tsohon mai kula da gidan yari, wanda ya sa ido kan yadda aka hallaka kimanin mutane 15,000 a wata shari’ar farko da aka gudanar a kasar Cambodia. bayan ya daukaka kara.


Shugaban kotun, Kong Srim yace kotun koli ta yanke wa Kaing Guek Eav hukuncin daurin rai da rai a gidan yari saboda rawar da ya taka wajen aikata munanan laifuka kan bil adama.

A shekarar 2010 aka yanke wa Kaing Guek Eav, da aka fi sani da Duch, daurin shekaru 30, sai dai ya daukaka kara, amma yanzu alkalan suka ce hukuncin da aka yanke ma shi a baya ya yi kadan, idan aka kwatanta da laifukan da ya aikata.