Isa ga babban shafi
MDD-Google

Google zai hada muhawara tsakanin Ban Ki-moon da Matasan Duniya a Intanet

A yau Talata, Kamfanin Google zai hada wata muhawara tsakanin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, da matasa a fadin duniya kai tsaye, ta hanyar sadarwa ta bidiyo a Intanet.

Sakatare Janar Na Majalisar Dinkin Duniya  Ban Ki-moon lokacin da yake jawabi a taron manema labarai tare da Fira ministan  Malaysia Najib Razak a Kuala Lumpur
Sakatare Janar Na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon lokacin da yake jawabi a taron manema labarai tare da Fira ministan Malaysia Najib Razak a Kuala Lumpur REUTERS/Samsul Said
Talla

Dex Torricke-Barton, kakakin kamfanin Google yace da misalin karfe 7:30 na yamma Agogon GMT za’a fara tattaunawar a shafin zumunta na Google+ tare da nuna muhawarar ta adireshin youtube.com/unitednations.

A cewar Mista Torricke-Barton, Ban Ki-moon daga Hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya zai zanta da matasa daga Nahiyar Turai da Asiya da Yankin Gabas ta tsakiya da Afrika da yankin Latin da Amurka inda za’a basu damar yin tambayoyi game da batutuwan da suka shafi rayuwarsu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.