Isa ga babban shafi
Nepal

Mutane 19 sun mutu a hadarin jirgin Nepal

Kimanin mutane 19 ‘Yan yawon bude ido, suka mutu a wani hadarin jirgin sama a kasar Nepal, cikinsu harda ‘Yan kasar Birtaniya bakwai, da ‘Yan kasar Sin biyar. Hadarin ya auku ne da sanyin safiyar yau Juma’a a kusa da tsaunin Mount Everest, inda jirgin ya fado ya kuma kama da wuta, jim kadan bayan ya tashi zuwa garin Lukla. 

Wani jirgi da ya fadi a yankin kasar Nepal
Wani jirgi da ya fadi a yankin kasar Nepal
Talla

Wadanda aka yi abin akan idonsu sun tabbatarwa da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, sunji mutane na kara a cikin jirgin kamin ya fado kasa, a yayin da hukumomin kula da tashin jirage su ka tabbatar da cewa matukin jirgin, ya aiko da sakon cewa sun yi karo da tsuntsu bayan sun tashi.

Dubban mutane ne su ka garazaya wajen da jirgi ya fadi, inda aka rawaito wasunsu na ta tafka kuka ganin abin da ya faru.

“Ga dukkan alamu, matukin jrgin ya yi kokarin ya saukar da jirgin a cikin kogi ne, amma kuma sai jirgin ya kama da wuta.” Wani mai Magana da yawun ‘Yan sanda, Binod Singh ya ce.

Wannan hadarin jirgin shi ne na shida a kasar ta Nepal a cikin shekaru shida da su ka gabata, inda hadari na karshe kamin wannan ya kashe mutane 15 a watan Mayu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.