Isa ga babban shafi
Venezuela

Shugabannin Duniya sun mika sakon Ta’aziyar rasuwar Chavez

Shugabannin kasashen Duniya sun mika ta’aziyararsu ga mutanen kasar Venezuela bayan mutuwar shugaba Hugo Chavez, Kasar Amurka ta bayyana fatar sabunta hulda da Venezuela mai arzikin man fetir bayan kwashe shekaru suna adawa da juna karkashin jagorancin Chavez.

Hugo Chávez  na Venezuela
Hugo Chávez na Venezuela REUTERS/Jorge Silva/Files
Talla

Chavez ya mutu yana da shekaru 58 sanadiyar cutar Cancer.

Kasar Cuba ta bayyana zaman makoki na kwanaki uku saboda rasuwar amininta Chavez, wanda kasar ta bayyana a matsayin Da ga tsohon shugaba Fidel Castro.

Shugaba Dilma Roussef ta Brazil ta bayyana Chavez a matsayin Gwarzo mai gwagwarmaya a yankin Latin Amurka.

Shugaba Evo Morales na Bolivia, yace mutuwa ta murkushe masa aboki.

Shugaban Ecuador, Rafael Correa, ya bayyana Chavez a matsayin gwarzo da samun irinsa ke da wahala.

Shugabanin kasashen Chile, Sebastine Pinera, da na Uruguay, Jose Mujica, da na Colombia, Juan Manuel Santos, da na Honduras, Porfirio Lobo, duk sun bayyana kaduwar su da rasuwar.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi jinjina ga takwaransa Hugo chavez wanda ya bayyana a matsayin shugaba jarumi tare da gode wa Chavez ga gudunmuwar da ya bayar wajen inganta dangantakar da ke tsakanin Rasha da Venezuela.

Bayan mika sakon ta’aziyarar shi ga mutuwar Chavez, Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad ya yi zargin makiya ne suka sa wa shugaban cutar Cancer.

Shugaba Ahmadinejad yace duniya ta yi rashin shugaba jarumi.

An kwashe shekaru Kasashen Iran da Venezuela suna adawa da manofofin Amurka wanda ya sa kasashen suka kulla kawance mai karfi a tsakaninsu.

Chavez ya kai ziyara kasar Iran sau 13 tsakanin shekarar 1999 zuwa kafin ya mutu, inda kuma Ahmadinejad ya kai ziyara kasar Venezuela sau 6 zuwa shekarar 2005.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.