rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Cambodia

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaban Khmer Rouge Leng Sary ya mutu

media
Shugaban Khmer Rouge Ieng Sary ya mutu Wikipedia

Leng Sary Tsohon Minsitan harakokin wajen kungiyar Khmer Rouge da ke adawa da gwamnatin Cambodia ya mutu yana da shekaru 87 wanda ake zargi da aikata laifukan yaki bayan kisan mutane sama da Miliyan a yakin Cambodia tsakanin shekarun 1975-1979.


A shekarar 1975 ne Leng Sary suka kafa gwamnatin Khmer Rouge bayan kaddamar da yakin basasa domin adawa da gwamnatin Cambodia a wajajen 1960.

Leng Sary shi ne babban jagoran kafa gwamnatin Khmer Rouge wanda ya rike mukamin Mataimakin Fira Minista da mukamin ministan harakokin waje a tsakanin 1975 zuwa 1979 kafin kargame shi a gidan yari a 1996.

Wata Kotu ta musamman da aka kafa domin sauraren karar Leng Sary ita ce ta bayar da sanarwar mutuwar shi a ranar Alhamis bayan ya kwashe mako guda a gadon Asibiti.

Daga cikin wadanda ake tuhuma da aikata laifukan yaki sun hada da Nuon Chea da tsohon shugaban kasa Khieu Samphan wanda shi ma ke jinya a Asibiti.