Isa ga babban shafi
Syria-G8-Korea

Rikicin Syria da Korea ne ya mamaye taron G8

Batun rikicin Syria da Korea ta Arewa shi ne zai mamaye taron Ministocin manyan kasashen 8 masu karfin tattalin arzikin duniya da ake gudanarwa a birnin London. A yau Alhamis ‘Yan tawayen Syria sun yi nemi Amurka ta taimakawa masu da makamai.

Gungun wakilan kasashe 8 masu karfin tattalin arzikin kasashen duniya
Gungun wakilan kasashe 8 masu karfin tattalin arzikin kasashen duniya Reuters
Talla

Wasu manyan kasashen Yammci da wasu kasashen Yankin Gabas ta tsakiya da ke yunkurin taimakawa ‘Yan tawaye domin kawo karshen mulkin Bashar al Assad za su gana a kasar Turkiya a ranar 20 ga watan Afrilu, kamar yadda wata majaiyar Diplomasiya ta tabbatar a taron kasashe 8 masu karfi tattalin arzikin duniya.

Majiyar tace sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry yana cikin wadanda za su halarci taron na kawayen Syria a birnin Istanbul.

Wani batu da zai ja hankalin taron na G8 da suka hada da Amurka da Birtaniya da Faransa da Jamus da Italia da Japan da Canada da kuma Rasha shi ne Barazanar yaki da ke fitowa daga Korea ta Arewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.