rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Ilimi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shafukan zumunta sun zama dandalin ‘Yan siyasa -bincike

media
Shugaban kasashen Duniya, Barack Obama na Amurka da Hollande na Faransa da Merkel ta Jamus AFP

Wani sakamakon bincike da aka gudanar ya gano shafukan zamunta a Intanet irin su Facebook da Twitter sun zama dandalayen da ‘Yan siyasa ke yada manufarsu musamman a kasar Amurka. Binciken yace akalla kashi 39 na Amurkawa sun abka siyasar Amurka ta hanyar mu’amula da ‘Yan siyasa a lokacin yakin neman zaben kasar a 2012, Kamar yadda wata cibiyar bincike ta Pew ta ruwaito.


Binciken yace kashi 26 na Amurkawa ke mu’amula da shafukan zumunta kafin a buga gangar siyasar Amurka a 2008.