rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Sri Lanka Renon Ingila David Cameron

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wasu shugabanni sun kauracewa taron kasashen renon Ingila

media
Mutanen Tamil suna rike da hotunan 'Yan uwansu da suka mutu a lokacin Sri Lanka da mayakan Tamil Tigers. REUTERS/Stringer

An bude taron kasashen renon Ingila da ake kira Commonwealth amma wasu shugabannin kasashen kungiyar da suka hada da Firaministan India da Canada sun kauracewa taron saboda laifukan yaki da suke zargin hukumomin kasar Sri Lanka sun aikata a lokacin rikicinsu da ‘Yan tawayen Tamil Tigers.


Bayan bude taron a Colombo babban birnin kasar Sri Lanka, Firaministan Birtaniya David Cameron ya kai ziyara yankin arewacin Jaffna inda dubban mutane suka rasa rayukansu a rikicin kasar na 2009 tsakanin gwamnatin Sri Lanka da ‘Yan tawayen Tamil Tigers.

Mista Cameron shi ne shugaba na farko daga Turai da ya kawo ziyara kasar Sri Lanka tun lokacin da Sri lanka ta samu ‘Yancin kai daga Birtaniya a shekarar 1948.

Shugaban Sri Lanka Mahinda Rajapakse, wanda ke fuskantar matsin lamba daga al’ummar kasar yana fatar yin amfani da taron ne domin nunawa duniya ci gaban da ya samar a kasar shi.

Shugaban kasashen Canada da India da Mauritius tuni suka bayyana matakin kauracewa taron na Commonwealth saboda laifuka yaki da suke zargin gwamnatin Mahinda Rajapakse, ta aikata.

Alkalumman tattalin arzikin Sri Lanka sun ce an samu ci gaba da kashi 8.2 kuma sama da Mutane miliyan biyu ne ‘Yan yawon bude ido suka kawo ziyara a kasar Sri Lanka a bara.

Yankin Jaffna nan ne aka gwabza yaki da ‘Yan tawayen Tamil Tigers, inda akalla rayukan mutane sama da 100,000 suka salwanta a rikicin da aka fara a 1972.

Cameron wanda ya kai ziyara a yankin ya jaddada bukatar lalle ya kamata a gudanar da bincike game da rikicin kasar da ya kawo karshe a 2009.