rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ilimi Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Google ya sayar da Motorola

media
Kamfanin Motorola mallakar Kamfanin Google REUTERS/Mike Stone/Files

Kamfanin Fasaha na Google ya sayar da bangaren kamfaninsa na Motorola ga kamfanin kasar China Lenovo akan kudi da suka kai dala biliyan 2.91 bayan Google ya kasa samun riba ga kamfanin na Motorola day a sa akan kudi dala Biliyan 12.5


Wannan shi ne ya kawo karshen kamfanin Google na mallakar kamfanin wayar salula.

Sai dai sayen Kamfanin na Motorola da kamfanin Lenovo ya yi, hakan ya dan girgiza hannayen jarin kamfanin a Hong Kong saboda fargabar riba daga ‘yan kasuwa.

Irin wannan ne ya shafi kamfanin google domin hammaya da kamfanonin kera wayoyin salula na zamani irinsu Samsung da Apple.