Isa ga babban shafi
Amurka

An samu surukin Osama da aikata laifukan ta’adanci

Wata Kotun birnin New York ta samu surukin Osama bin Laden da aikata laifukan ta’addanci da suka shafi hada baki domin kisan Amurkawa tare da taimakawa kungiyar al Qaeda. An kwashe tsawon mako uku ana sauraren karar Suleiman Abu Ghaith, wanda ke wa’azi a kasar Kuwait.

Sulaiman Abu Ghaith surukin Marigayi Osama Bin Laden
Sulaiman Abu Ghaith surukin Marigayi Osama Bin Laden REUTERS/Handout
Talla

An bayyana Abu Ghaith a matsayin na hannun damar Osama bin Laden wanda ke auren babbar ‘yarsa kuma mutumin da ke tsayawa a kusa da shi a cikin wani hoton bidiyo da Osama ya yi ikirarin daukar alhakin kai harin watan Satumba.

Yanzu Abu Ghaith zai fuskanci hukuncin daurin da rai a gidan yarin Amurka, amma lauyan da ke kare shi yace zai daukaka kara bayan ya kalubalanci hukuncin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.