rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rasha Kazakhstan Belarus

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rasha da Belarus da Kazakhstan sun kulla yarjejeniya

media
Shugabannin kasashen Rasha da Belarus da Kazakhstan a taron kulla yarjejeniyar kafa kungiyar Tattalin arzikinsu REUTERS/Mikhail Klimentyev/RIA Novosti/Kremlin

Kasar Rasha ta kulla yarjejeniya tsakaninta da Belarus da Kazakhstan game da kafa babbar kungiyar tattalin arziki ta Eurasian tsakanin kasashen guda uku na tsohuwar daular Soviet domin karo da kungiyar Tarayyar Turai. Shugaban Rasha Vladimir Putin da shugaban Belarus Alexander Lukashenko da shugaban Kazakhstan Nursultan Nazarbayev sun amince da yarjejeniyar ne a Astana babban birnin Kazakhstan.


A watan Janairun shekarar 2015 ne kungiyar kasashen ta Eurasia zata fara aiki, da aka tsara domin inganta huldar kasashe na tsohuwar daular Soviet. Kodayake ban da kasar Ukraine da al'ummar kasar suka rabu gida biyu, masu da'awar Turai da Rasha.