rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Cambodia

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Cambodia: Mutane uku sun mutu wajen ceto Kare a Rijiya

media
Kare yana tafiya a saman titi tare da Jami'in tsaro David Cruchon/Flick'r/CC

‘Yan sandan kasar Cambodia sun tabbatar da mutuwar mutane Uku a cikin Rijiya a gabacin kasar a lokacin da suke kokarin ceto rayuwar wani Kare da ya fada a cikin rijiyar. Al’amarin ya faru ne a yankin Kratie a jiya Assabar inda wani Matashi  mai suna Say Phalla dan shekaru 25 ya fara fadawa a cikin rijiyar mai zurfin kafa 32 bayan karensa ya fada a ciki.


Daga nan ne kuma mahaifiyar shi da wani makwabcinsu suka abka cikin rijiyar domin tsamo Phalla da ya fada a rijiyar don ceto Karen shi.

‘Yan sanda sun yi nasarar tsamo gawawwakin mutanen da kuma gawar Karen daga cikin rijiyar bayan sun samu labarin faruwan al’amarin.