Isa ga babban shafi
Cambodia

Shugabannin Khmer Rouge sun aikata laifukan yaki

Kotun Hukunta laifufukan yaki da ke samun goyan bayan Majalisar Dinkin Duniya da ke zama a Cambodia ta samu wasu manyan shugabanin kungiyar Khmer Rouge biyu da aikata laifufukan yaki tare da yanke masu hukuncin daurin rai da rai.

Tsohon Shugaban Khmer Rouge Khieu Samphan.
Tsohon Shugaban Khmer Rouge Khieu Samphan. Reuters/Mark Peterson/ECCC
Talla

Nuon Chea wanda ya rike mukamin mataimakin shugaba Pol Pot da Khieu Samphan shugaban kasa a karkashin gwamnatin Khmer Rouge na daga cikin shugabanin da aka samu da laifi saboda mutuwar akalla mutane miliyan biyu a karkashin mulkinsu daga shekara ta 1975 zuwa 1979.

Lauyoyn da ke kare shugabannin sun ce zasu kalubalanci hukuncin akan laifukan kisa da cin zarafin bil’adama da Kotun ta kama shugabannin da aikatawa.

Kungiyar Tarayyar Turai ta yaba da hukuncin da aka yanke wa shugabannin na Khmer Rouge.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.