An Zartas da dauri na shekaru 3 kan wata Mace don kalubalantar Sarkin Kuwait
Kotu a kasar Kuwait ta daure wata mata tsawon shekaru uku gidan yari saboda ta soki Sarkin kasar Sheikh Sabah al-Ahmad Sabah a wajen wani taro a bainin jama'a.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Matar mai suna Rana Jassen al-Saadun wadda ‘yar rajin kare hakkokin mata ce, ta gargadi Sarkin ne da kada ya kuskura ya amince da gyaran kundin zabe domin Gwamnati ta ci gaba da rike majalisa.
Yanzu haka akwai wani jagoran ‘yan adawa a kasar Mussallam al-Barrak wanda aka zartas masa da hukuncin dauri gidan maza a shekara ta 2012 saboda irin wannan laifi..
Ita dai Rana Jassen al-Saadun ba ta kasar a lokacin da kotun ta zartas da hukuncin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu