Isa ga babban shafi
IMF

Lagarde na son yin tazarce a IMF

Shugabar Hukumar bayar da lamuni ta duniya Christine Lagarde tace tana nazarin bayyana aniyarta na sake takarar kejerar shugabancin hukumar a wa’adi na biyu idan aikinta ya kare a watan Yuli na shekara mai zuwa. Lagarde ta shaidawa manema labarai cewar idan kasashen da suka mallaki bankin sun gamsu da rawar da ta taka to za ta sake takara a shekara mai zuwa.

Shugabar IMF Christine Lagarde
Shugabar IMF Christine Lagarde Reuters/路透社
Talla

Tsohuwar ministan kudin Faransa ta sha fuskantar suka daga kasashe matalauta da masu tasowa kan yadda bankin ba ya tausayinsu.

Babban kalubalen da ke gaban Largarde shi ne batun cim ma yarjejeniya da Girka da ke barazanare ficewa daga kasashen da ke amfani da takardar kudin yuro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.