rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ireland Auren jinsi Amurka Mexico Chile

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An yi bikin murnar auren jinsi guda a Ireland

media
Wasu masu auren jinsi guda REUTERS/Carol Tedesco

A Jamhuriyar Ireland, Dubun bubatan jama’a ne suka mamaye titunan Dublin, babban birnin Kasar inda suka gudanar da gagarumin bikin nuna farin ciki da kuma alfahari cewa Kasar ce ta farko a duniya da ta fara kada kuri’ar raba gardama akan auren jinsi guda.


Kimanin kashi 62 cikin 100 ne na al-ummar kasar suka goyi bayan yin auren jinsi gudan a kuri’ar.

Wannan na zuwa ne bayan Kotun kolin Amurka ta halatta auren jinsi guda a jihohi hamsin na Kasar.

A bangare guda, wasu 'yan kasashen yankin latin Amurka daya hada da Chile da Mexico sun yi pareti a jiya asabar , inda suka bukaci hukumomi da su basu cikakken 'yancin auren jinsi kamar yadda Amurka ta yi a ranar jumma’ar data gabata.